Bankin Duniya ya bayyana cewa farashin man fetur a Nijeriya ya ƙaru da sama da kashi 50 tun bayan ɓarkewar rikicin Iran, lamarin da ke ƙara tsananta hauhawar farashi da kuma matsin rayuwa ga al’umma.
Babban masanin tattalin arziki na Bankin Duniya a Najeriya Fiseha Haile ne ya bayyana hakan, yayin gabatar da rahoton man fetur a birnin Abuja.
Ya ce duk da cewa harkokin kasuwanci na ci gaba da bunƙasa, tashin farashin makamashi na ƙara haifar da hauhawar farashi a fannoni daban-daban na tattalin arziki.
A cewar rahoton da ya gabatar, hauhawar farashin mai ya jawo ƙarin tsadar sufuri, abinci da samar da kayayyaki, inda farashin dizal ma ya kusan ninkuwa a kasar.
Jaridar Daily Trust ta ambato Fiseha Haile ya na gargadi cewa ci gaba da hauhawar farashi na iya kawo barazana ga kudaden shiga da kokarin rage talauci, inda ya ba da shawarar a sassauta takunkumin shigo da man fetur domin rage matsin farashi.
Duk da wannan ƙalubale, Bankin Duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai bunƙasa da kusan kashi 4.2 cikin ɗari a shekarar nan ta 2026.
Bankin ya shawarci masu tsara manufofi su ci gaba da tsaurara manufofin kuɗi, su adana ribar da ake samu daga mai, tare da kauce wa dawo da tallafin mai gaba ɗaya domin rage hauhawar farashi.
A nasa ɓangaren, daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis ya jaddada cewa gyaran ɓangaren makamashi shi ne mafita mafi muhimmanci domin bunƙasa tattalin arziki, yana mai gargadin cewa burin Najeriya na gina tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya na iya gagara idan ba a gyara tsarin wutar lantarki ba.
Ya kuma buƙaci a ƙarfafa tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati tare da haɗin kai tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya wajen samar da muhimman ayyukan more rayuwa ga ‘yan kasar.
