Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuFarfesoshin Nijeriya na cikin jerin na nahiyar Afrika da ba su da...

Farfesoshin Nijeriya na cikin jerin na nahiyar Afrika da ba su da albashi mai kyau

Bayanan da jaridar Punch ta tattaro sun ce malamin jami’a a Nijeriya da ya kai matakin farfesa na samun matsakaicin albashi na dala 366 (kimanin Naira 500,000) a wata, wanda ya yi kasa kwarai da na takwarorinsu a wasu kasashen nahiyar.

Bayanan da suka shafi albashin farfesoshi a jami’o’in gwamnati na nahiyar Afrika sun bayyana cewa yayin da farfesa a Nijeriya ke samun kusan dala 4,400 a shekara, farfesa a Afirka ta Kudu na samun dala 57,471 a shekara, wanda ya ninka fiye da sau 13.

Uganda na biye da dala 50,595 a shekara, sai Kenya da dala 48,000 a shekara, yayin da ƙasashen da tattalin arzikinsu bai kai na Nijeriya ba, irin su Eswatini (dala 41,389), Lesotho (dala 32,455), da Gabon (dala 29,907), suke biyan albashin farfesoshi a shekara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata