Friday, April 10, 2026
HomeKetareFitacciyar 'yar jarida kuma mai fafitika a shafukan sadarwa Samira Sabo, ta...

Fitacciyar ‘yar jarida kuma mai fafitika a shafukan sadarwa Samira Sabo, ta yi fatan ganin an saki hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum

‘Yar jarida a Nijar wacce ta yi fice a baya wajen sukar gwamnatin jamhuriyar ta 7 ta tsohon shugaban kasa Issoufou Mahamadou da magajinsa Mohamed Bazoum ta ziyarci gidan shugaba Issoufou Mahamadou domin taya shi murnar sakin abokan gwagwarmayar siyasarsa. 
Samira a cikin sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce watanni biyu da suka gabata ta samu ganawa da tsohon shugaban kasar inda ta bukaci da ya shiga cikin lamarin siyasar kasar domin samar da mafita akan dambarwar siyasar da ake ke ciki.
‘Yar jaridar ta ce a nata ra’ayi, mataki na gaba ya kasance na sakin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum tare da tattaunawa da magoya bayansa har ma wadanda suke hijira a ketare.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata