Tsohon shugaban jam’iyyar APC na Nijeriya Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa, tare da wasu manyan ‘yan siyasa sun goyi bayan Murtala Sule Garo ya zama mataimakin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Doguwa ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar sa, an cimma matsayar ne bayan tattaunawa tsakanin jagorori da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC.
Ya kuma ce kaso 90 na wadanda suka halarci zaman tattaunawar sun goyi bayan Murtala Sule Garo, yana mai kira ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya duba lamarin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
