Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuGirmama Marigayi Buhari da Tinubu ya yi ne ya sa za mu...

Girmama Marigayi Buhari da Tinubu ya yi ne ya sa za mu goyi bayansa a 2027 – Sarkin Daura

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin sake tsayawa takara a zaben 2027, yana mai cewa yadda Shugaban Ƙasar ya nuna halin dattako da girmamawa ga marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da cancantar Tinubu ya ci gaba da shugabanci.

Sarkin ya bayyana haka ne a fadarsa da ke Daura, yayin da yake karɓar tawagar uwargidar Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, tare da matan wasu gwamnoni daga sassan ƙasar nan, da suka kawo masa ziyara ta ta’aziyya.

A cewar rahoton Premium Times, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ne ya jagoranci tawagar zuwa Daura domin isar da saƙon gaisuwa da jimami ga iyalan marigayi Buhari.

Sarkin Daura ya bayyana matuƙar jin daɗinsa da yadda Tinubu ya bai wa marigayi Buhari girmamawa ta musamman a lokacin jana’izarsa, yana mai cewa hakan alama ce ta shugabanci na adalci, kima da mutuntawa, wanda ke kara tabbatar da nagartar Tinubu wajen jan ragamar Nijeriya.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata