Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedGwamatin Nijeriya ta kaddamar da kwamitocin yaki da ambaliya

Gwamatin Nijeriya ta kaddamar da kwamitocin yaki da ambaliya

A Larabar nan ne ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli Farfesa Joseph Terlumun Utsev ya kaddamar da wani kwamitin kwararru da zai samar da dabarun daƙile afkuwar ambaliyar ruwa a fadin kasar nan.
Kwamitin zai yi aikin samar da taswirar inganta madatsun ruwa da tsarin zamantakewa da ma wasu karin shirye-shiryen inganta muhalli cikin gaggawa. 
Tun da farko, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da wasu muhimman tsare-tsare guda biyu da suka haɗa da kafa asusun bayar da agajin Ibtila’i da samar da kwamitin yaki da ambaliya ruwa . 
Wadanda suka halarci taron Kaddamar da kwamitin sun hada da 
Ministan Watsa Labarai, Muhammad idris da na Kasafin Kudi sanata Abubakar Atiku Bagudu, da minista Muhalli Balarabe Abbas inda dukansu suka jaddada bukatar ganin Kwamitin ya fara aiki nan take.
 
Kazalika gwamatin Shugaba Tinubu ta ware kudaden tallafin yaki da Ibtila’in ambaliyar ga ilahirin jihohin kasar 
Wannan matakin ya nuna yadda gwamnati ta himmatu wajen shawo kan iftila’in ambaliyar ruwa da samar da kariya ta dindindin.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata