DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeUncategorizedGwamna Zulum na jihar Borno ya kaddamar da raba tallafin tireloli 100...

Gwamna Zulum na jihar Borno ya kaddamar da raba tallafin tireloli 100 na abinci daga Shugaba Tinubu

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya fara rabon tireloli 100 na kayan abinci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba wa mazauna Jihar Borno. An fara rabon kayan abincin, wanda ya kunshi masara, gero, da dawa, ga gidajen da suka fi bukata a Gamboru, Ngala, da wasu al’ummomi da aka kebe saboda mamakon ruwa da ambaliyar da suka shafe watanni hudu.
Da yake magana yayin kaddamar da rabon kayan, Gwamna Zulum ya jaddada muhimmancin tallafin wajen rage wahalhalun da al’ummar suka fuskanta, sannan ya gode wa Shugaba Tinubu da hukumomin tarayya da suka bada gudummawa. Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bayar da karin tireloli 100 na shinkafa domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.
Zulum ya bayyana cewa gwamnatinsa tana ci gaba da sauya matsaya daga rabon kayan abinci zuwa samar da hanyoyin dogaro da kai, ciki har da kafa tsarin ban ruwa domin noma na tsawon shekara a cikin al’ummomin da aka sake tsugunar da su, musamman a Ngala.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata