Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaGwamnan Jigawa ya yi girgiza a majalisar kwamishinoninsa

Gwamnan Jigawa ya yi girgiza a majalisar kwamishinoninsa

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanar da sauye-sauyen mukamai a cikin Majalisar Zartaswa ta jiha, a wani yunkuri na inganta aiki da daidaita tsarin mulki.

A cikin sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana cewa:

– Hon. Muhammed Alhassan, da ya kasance Kwamishinan Ma’aikatar Gidaje, An mayar da shi zuwa Ma’aikatar Ruwa.

– Hon. Ibrahim Garba Hannun Giwa, da yake Kwamishinan Ruwa, yanzu zai jagoranci Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Ci gaban Al’umma.

– Hon. Ahmed Garba (MK), wanda ya ke Kwamishinan Kananan Hukumomi, an tura shi zuwa Ma’aikatar Gidaje, Tsare-Tsaren Birane da Cigaban Yankuna.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa wadannan sauye-sauyen sun fara aiki daga wannan Litinin din, 5 ga Mayu, 2025, kuma an umurci dukkan kwamishinonin da su karɓi sabbin ofisoshinsu kafin Litinin, 19 ga Mayu, 2025.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata