Tuesday, April 7, 2026
HomeUncategorizedGwamnan jihar Kano Engr. Abba Yusuf ya sanya hannu kan dokar...

Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta jihar

 

Abba Kabir Yusuf/Aminu Abdussalam

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a kan dokar ne a yayin zaman majalisar zartaswa ta jihar da ya gudana a ranar Talata 18/2/2025.

Hakan na zuwa ne makwanni biyu bayan majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da kuduri bayan yin mahawara mai zurfi akan kudurin.

A cikin wasu tanade tanaden dokar, ta baiwa rundunar tsaron damar yakar miyagun laifuka, za kuma su gudanar da ayyukansu a fadin jihar.

Sanya hannu kan dokar shi ne mataki na karshe na tabbatar da ita a hukumance yayin da ake sa ran hukumomi za su sanar da tsarin daukar ma’aikatan rundunar, da kuma nadin wadan da za su jagoranci rundunar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata