Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedGwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya haramta sanya dalibai aiki mai tsauri...

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya haramta sanya dalibai aiki mai tsauri a cikin makarantu

Abba Kabir Yusuf

Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya yi gargadi ga malaman makarantu da kada su umurci dalibai yin ayyuka masu tsauri a ciki ko wajen makaranta.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ga manema labarai.

Gwamnan ya jaddada cewa makarantu wajen ba da ilimi ne da jagoranci, kyautata ɗabi’a ba wajen bautar da dalibai ba.

A wata ziyarar bazata da gwamnan ya kai wata makarantar koyar da larabci da ke Kano, ya tarar da dalibai su na aiki mai wahala a cikin makarantar .

A bayyane gwamnan ya nuna rashin jin daɗi, tare da  tambayar shugaban makarantar game da sanya dalibai irin waɗannan ayyuka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata