Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa tana tattaunawa da hukumomin Amurka kan barazanar soja da shugaban Amurka Donald Trump ya yi mata.
Ministan labarai da wayar da kan jama’a Alhaji Mohammed Idris ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da Sky News, inda ya ce ana samun ci-gaba ta hanyar diflomasiyya wajen daidaita dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.
Idris ya bayyana cewa wasu daga cikin bayanan da Amurka ke dogaro da su na da rauni, saboda rashin fahimtar yadda matsalar tsaro da bambancin ƙasar ke da sarkakiya.
Haka kuma ya musanta cewa Nijeriya ta rasa wani yanki ga ‘yan bindiga, yana mai cewa hakan ba gaskiya bane.
A cewar sa, Amurka ta kasance abokiyar haɗin gwiwa wajen yaƙi da ta’addanci, yana mai kira da ta ci-gaba da taimakawa domin samar da zaman lafiya a ƙasar.
