Tuesday, April 7, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnatin APC na amfani da talauci a matsayin makamin hana 'yan Nijeriya...

Gwamnatin APC na amfani da talauci a matsayin makamin hana ‘yan Nijeriya su juya mata baya – Zargin Atiku, El-rufa’i, da Amaechi

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, sun caccaki gwamnatin shugaba Bola Tinubu saboda amfani da talauci a matsayin makami ga ‘yan Nijeriya.

Jiga-jigan siyasar na jawabi ne a wani da aka gudanar don taya Amaechi murnar cika shekaru 60 a Abuja.

A cewar Atiku, gwamnati tana amfani da talauci a matsayin makami don tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya ba su juya musu baya ba.

Sh kuwa El-Rufai, yace Najeriya na cikin wani mawuyacin hali da bata taba shiga ba tun 1914.

A gefe daya kuwa, Amaechi yace manufofin gwamnatin Tinubu na cika aljihun wasu mutane kalilan ne a cikin gwamnati.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata