Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnatin Kano ta saki fursunoni mata 8 daga gidan gyara hali ciki...

Gwamnatin Kano ta saki fursunoni mata 8 daga gidan gyara hali ciki har da masu juna biyu

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi wa fursunonin afuwa ne a lokacin da ya kai ziyarar ba zata a gidan gyaran hali, tare da rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa makasudin ziyarar shi ne duba halin da fursunonin ke ciki da kuma lalubo hanyoyin da gwamnatin jihar za ta tallafa wa jin dadinsu.

Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yawan fursunonin da ke jiran shari’a, inda ya ce daga cikin fursunoni 1,939, mutum 382 ne kawai aka yanke musu hukunci, yayin da 1,536 ke jiran shari’a.

Ya kuma ba da tabbacin cewa jihar za ta hada kai da bangaren shari’a domin a gaggauta yi musu da kuma rage cunkoso a gidan gyaran halin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata