Thursday, April 9, 2026
HomeUncategorizedGwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da zaman makoki na kwana uku...

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da zaman makoki na kwana uku bayan ‘yan ta’adda sun yi ajalin mutum 44 a masallaci

Abdoulrahmane Tiani

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da zaman makoki na kwana uku a kasar  bayan ajalin wasu mutane 44 a kudu maso yammacin ƙasar a wani hari da ake zargin “yan ta’adda” da ke da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh suka kai.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar Nijar ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a gidan talabijin na ƙasar a ranar Juma’a.

Ma’aikatar ta ce ‘yan ta’addan sun yi ajalin mutanen ne a lokacin da suka afka cikin wani masallaci a ƙauyen Fombita da ke Kokorou inda suka far wa masallata.

Ma’aikatar ta yi Allah-wadai da harin tare da shan alwashin ƙara matsa ƙaimi domin yaƙi da ta’addanci a yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata