Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnatin Najeriya na shirin sake ciyo bashin dala biliyan 1.75 daga bankin...

Gwamnatin Najeriya na shirin sake ciyo bashin dala biliyan 1.75 daga bankin duniya

Gwamnatin tarayyar Nijeriya na shirin sake ciyo bashin dala biliyan 1.75 daga bankin duniya duk da samun karuwa a kudaden shiga da kaso 40 a cikin watanni takwas na shekarar 2025, kamar yadda binciken jaridar punch ya nuna.

A ranar Laraba fadar shugaban Najeriyar ta bayyana ci gaban da ta ce ta samu a kudaden shiga daga bangarorin da ba na man fetur ba.

Sai dai binciken na Punch ya bayyana cewa akwai wuraren muhimman ayyuka da ke bukatar a cike musu gibi, musamman ayyukan gine-gine, bayan da kungiyar ‘yan kwangila’ yan asalin Najeriya suka gudanar da zanga-zangar neman a biya su basukan da suke bi tun shekarar 2024, wanda adadin su ya doshi Naira Tiriliyan 4.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata