Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnatin Nijeriya na shirin ciyo bashin dala miliyan 238 daga Japan

Gwamnatin Nijeriya na shirin ciyo bashin dala miliyan 238 daga Japan

Gwamnatin Nijeriya tana tattaunawa da Japan International Cooperation Agency (JICA) kan rancen dala miliyan 238 domin faɗaɗa hanyar sadarwar wutar lantarki ta ƙasa, musamman ɓangaren rarraba wutar (transmission).

Wannan na daga cikin sakamakon abun da ya biyo bayan taron TICAD 9 da aka kammala a Yokohama, Japan, inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci tawagar Najeriya, tare da Ministan Wuta, Adebayo Adelabu, da wasu jami’an gwamnati.

Rahoton gidan talabijin na Channels yace rancen zai ginu ne a kan amincewar Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) da ta bayar a baya kan kuɗin haɗin gwiwa na naira biliyan 19, domin a samu damar karɓar rancen JICA na dala miliyan 238.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata