Gwamnatin Nijeriya ta bankado shirin wasu kamfanonin waje na kunyata Tinubu yayin ziyararsa a Birtaniya
Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano wani shiri da wasu kamfanonin hakar ma’adinai na kasashen waje ke yi domin bata wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu suna a lokacin ziyararsa ta kasa zuwa Birtaniya.
Ma’aikatar Ma’adinai ta kasa ta ce wani kamfani mai suna Jupiter Ltd na shirin kaddamar da wata manufa ta yada jita-jita da kuma daukar nauyin zanga-zanga domin kunyata shugaban kasa yayin ziyarar.
A wata sanarwa da mataimakin ministan ma’adinai kan harkokin yada labarai, Segun Tomori, ya fitar, ya ce kamfanin na shirin daukar nauyin kamfen na kafafen yada labarai domin sukar gwamnati kan matakan da take dauka wajen tsaurara dokokin hakar ma’adinai.
Ana sa ran shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar kwanaki biyu kasar Birtaniya tare da matarsa uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu.
Jaridar The Nation ta ruwaito wannan ita ce ziyarar kasa ta farko da Najeriya za ta kai a fadar Windsor cikin shekaru 37.
