Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnatin Nijeriya ta ce cin jarabawar lissafi “Mathematics” wajibi ne ga daliban...

Gwamnatin Nijeriya ta ce cin jarabawar lissafi “Mathematics” wajibi ne ga daliban Sakandare kafin kammalawa

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa lallai dukkan ɗalibai masu rubuta jarabawar kammala sakandare su cigaba da rubuta lissafi tare da harshen Turanci a matsayin wajibi.

Mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta Nijeriya Boriowo Folashade ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a Lahadinan.

A ranar Talata Boriowo ta sanar da cewa ɗaliban sashen fasaha da zamantakewa ba za a sake buƙatar lallai sai sun samu kiredit a lissafi ba kafin su samu gurbin karatu a jami’a ko kwalejin kimiyya sanarwar da ta jawo ce-ce-ku-ce tsakanin masana ilimi da jama’a.

Sai dai a sabon bayanin ta ce wannan gyara bai soke wajabcin ɗalibai su rubuta jarabawar lissafi da Turanci ba, illa dai ya ba jami’o’i damar karɓar ɗalibai zuwa wasu fannoni ko shirye-shiryen karatu da ba lissafi ko Turanci ke zama tilas ba.

A cewarta, wannan mataki na cikin shirin gwamnati na tabbatar da daidaito da ba kowa dama wajen samun ilimi, tare da bunƙasar ci-gaban ɗan Adam kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata