DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeUncategorizedGwamnatin Nijeriya ta fara biyan naira 77,000 alawus na wata-wata ga matasan...

Gwamnatin Nijeriya ta fara biyan naira 77,000 alawus na wata-wata ga matasan NYSC

Gwamnatin Nijeriya ta fara biyan naira 77,000 alawus na wata-wata ga matasan NYSC

Bayan jinkirin biyan sabon alawus din na naira 77,000, da Shugaba Tinubu ya amince da yin karin watanni shida da suka gabata, a yanzu matasan sun fara ganin sabon alawus din nasu.

A lokutan baya ana biyan masu yi wa kasa hidima alawus na naira 33,000, karin da aka yi tun a shekarar 2020 lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daya daga cikin masu yi wa kasa hidima a jihar kano Nkiruk ta shaida wa SolaceBase a ranar Laraba cewa, zuwa yanzu an fara biyan alawus din na naira 77,000 ga masu yi wa kasar hidima.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata