Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da matasa miliyan 20 daga...

Gwamnatin Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da matasa miliyan 20 daga yanzu zuwa shekarar 2030

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kaddamar da shirin horas da matasa da nufin samarwa matasa miliyan 20 damar samun aiki da hanyoyin kasuwanci daga yanzu zuwa shekarar 2030.

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ne ya sanar da hakan a taron farko na kwamitin gudanarwa na Generation Unlimited Nigeria da aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shettima, wanda shi ne shugaban kwamitin, ya bayyana cewa akalla kashi 60 na wadanda zasu amfana da shirin mata ne.

Ya ce tsarin ƙwarewar sana’o’in matasa a ƙasar na fuskantar manyan ƙalubale kashi uku kuma matasa da dama ba sa samun damar shiga shirye-shiryen domin samun horo.

Ya kuma ce babu isassun kayan aiki da za su basu damar samun horon cikin sauki.

RELATED ARTICLES

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata