Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedGwamnatin Nijeriya ta karbi kashin farko na kayan aikin noma daga kasar...

Gwamnatin Nijeriya ta karbi kashin farko na kayan aikin noma daga kasar Belarus

 

Bola Ahmad Tinubu

Gwamnatin tarayya ta karbi kashin farko na motocin noma 2,000 da sauran kayan aikin noma 9,027 daga kasar Belarus a wani bangare na kokarinta na habaka samar da abinci a kasar.

Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun, ne ya sanar da hakan a cikin wani faifan bidiyo da aka saka akan X.com ranar Talata.

A cewar Olusegun, za a raba sabbin kayan aikin noman ne a karkashin wasu muhimman tsare tsare guda uku da aka yi domin samar da ingantaaccen noma.

Ya ce shirin na da nupin samarwa da manoma sauki ta hanyar samun kayan aikin noma na zamani da baiwa kananan manoma damar yin hayar motocin domin suyi aiki a gonakinsu kamar yadda ake bukata

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata