DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeUncategorizedGwamnatin Nijeriya ta ware Naira biliyan 112 don tabbatar da tsaro da...

Gwamnatin Nijeriya ta ware Naira biliyan 112 don tabbatar da tsaro da kulawa a makarantun yara cikin shekaru uku masu zuwa

Shugaba Tinubu

Ministar harkokin mata, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba a Abuja domin tunawa da ranar yara ta duniya.

Ana bikin ranar yara a kowace shekara a duniya a ranar 20 ga Nuwamba, kuma rana ce da majalisar dunkin duniya ta ware domin ‘yancin yara. 

Sakamakon haka, majalisar dinkin duniya ta yi bikin a wannan rana tare da kokarin wayar da kan al’umma game da muhimmancin ilimin yara, kula da lafiyar su da kuma bukatar magance matsalolin da yaran ke fuskanta.

Ministar harkokin mata, don haka ta ce gwamnati ta himmatu wajen samar da yanayin da kowane yaro zai samu ilimi da lafiya da rayuwa ingantacciya ba tare da tsoro ko cutarwa ba.

A cewarta, an ba da tallafin ne ta hanyar sabon tsarin kula da makarantun yara tare da bayar da tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata