Gwamnatin Nijeriya ta shigar da karar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa zargin yin kutse kiran wayar mai ba Shugaba Tinubu shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.
Jaridar Punch ta rawaito cewa an shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CR/99/2026 a babbar kotun tarayya da ke Abuja.
A yayin wata hira da yayi El-Rufai ya bayyana cewa ya san mutanen da suka yi kutse a wayar Ribadu, amma bai kai rahoto ga hukumomin tsaro ba, abin da ya saba wa Sashi na 27(b) na dokar Cybercrimes ta 2024.
