Gwamnatin tarayya za ta gina titin jirgin ƙasa a cikin birnin Kano wanda kuɗinsa ya kai naira tiriliyan 1.5, a cewar shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar wakilai, Abubakar Kabir Abubakar Bichi.
Ɗan majalisar na Bichi ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Kano, inda ya ce aikin zai magance matsalolin sufuri a cikin birnin.
Ya ce sun ziyarci kasashen waje, musamman na Turai, inda suka ga irin waɗannan ayyuka kuma suka fahimci muhimmancinsu, yana mai cewa hakan zai ƙara bunƙasa tattalin arziƙin jihar idan aka kammala.
Ɗan majalisar na Bichi ya ce, sabanin hasashen da wasu ke yi, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da muhimman ayyuka da suka haɗa da samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, noma, ilimi da tsaro a arewacin Nijeriya.
