Gwamnatin tarayya za ta fara sayar da shinkafa 50kg akan kudi N40,000
A ranar Litininin ne gwamnatin tarayya ta sanar da raba karin motoci 10 cike da buhunan shinkafa 50kg ga kowace jiha. Wadannan buhuhuna za a siye su ne a wasu wurare na usamman akan Naira 40,000 kowanne.
A yayin taron majalisar, Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma na kasa Mohammed Idris, ya yi wa manema labarai karin haske kan shirin gwamnatin na rage radadin talauci da kuma yaki da tsadar rayuwa a kasar.
Majalisar zartaswa ta tarayya ta bayyana cewa, mafi yawan bukatun da masu zanga-zangar suka gabatar, tuni gwamnati ta biya su.
Don haka,yin zanga-zangar ba lallai ba ne, saboda gwamnati na aiki tuƙuru kan magance kalubalen da ake fuskanta.
Yace shugaban kasa ya ji damuwar wadanda ke shirya zanga-zangar kuma tuni ya fara daukar matakai a, domin gwamnati na kokarin tabbatar da wadatar abinci.
“A taron majalisar da ya gabata mun sanar da raba tireloli 20 na shinkafa ga gwamnonin jihohi ga masu bukata musamman marasa galihu a cikin al’umma”.
Idris ya bayyana cewa an kai shinkafar cibiyoyi daban-daban a fadin jihohin kasar nan, inda za a iya siyan ta kan Naira 40,000 kan kowacce buhu.

