Gwamnatin Tarayya ta ce ta riga ta bai wa ’yan Nijeriya sama da miliyan 34 masu rauni tallafin kuɗi a ƙarƙashin shirin conditional cash transfer, domin rage matsin tattalin arziki da talauci.
Ministan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Dr Bernard Mohammed Doro, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Calabar, Jihar Cross River, yayin taron farko na National Council on Humanitarian Affairs and Poverty Reduction.
Doro ya ce shirin na nuna ƙudurin gwamnatin Tarayya na fitar da miliyoyin ’yan Nijeriya daga talauci ta hanyoyin tallafi masu tsari, haɗin kai da dogaro da bayanai.
Ya ƙara da cewa gwamnati na da burin kai miliyan 50 kafin ƙarshen shekarar nan, inda ya jaddada cewa kariyar jin-ƙai na daga cikin ginshiƙan manufofin rage talauci na gwamnatin Tinubu.
