Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnatin Tinubu ta sa takunkumin kafa sabbin makarantun gaba da sakandare a...

Gwamnatin Tinubu ta sa takunkumin kafa sabbin makarantun gaba da sakandare a Nijeriya har nan da shekaru 7 masu zuwa

Gwamnatin Nijeriya ta sanya wa’adin dakatar da kafa sabbin jami’o’i, kwalejojin fasaha da na ilimi na tarayya na tsawon shekaru bakwai, bisa hujjar yawaitar cibiyoyin da ake amfani da su kasa da yadda ya kamata, karancin albarkatun da ake da su, da kuma raguwar ingancin ilimi.

An amince da wannan matakin ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya da aka gudanar ranar Laraba a fadar shugaban kasa, Abuja, karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, bayan gabatarwar da Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya yi.

Sai dai, duk da wannan takunkumi, Majalisar ta amince da kafa sabbin jami’o’i tara.

Da yake zantawa da ’yan jarida a fadar shugaban ƙasa bayan zaman, Alausa ya ce matsalar tsarin ilimi na manyan makarantu a Najeriya yanzu ba samun gurbi ba ce, sai dai yawaitar maimaita cibiyoyi marasa amfani yadda ya dace, ƙarancin gine-gine, rashin isassun malamai, da kuma raguwa a yawan ɗaliban da ke shiga a yawancin cibiyoyin da ake da su.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata