Gwamnatin Nijeriya ta bayyana damuwarta kan hukuncin da wata kotun tarayya da ke Canada ta yanke na bayyana wasu jam’iyyun siyasa a Nijeriya a matsayin ‘yan ta’adda.
A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta fitar ta yi kakkausar suka kan hukuncin kotun, kan batun cewa manyan jam’iyyun kasar nada alaka da ta’addanci, kuma ta ce wannan kwata-kwata karya ce kuma ba abin yadda bace.
Sanarwar ta ce Nijeriya kasa ce mai cin gashin kanta da ke da tsarin doka da tsarin mulki da ke tafiyar da harkokin siyasa, don haka jam’iyyun siyasarta suna aiki ne bisa tsarin doka kuma suna da mahimmanci ga dimokuradiyyar kasar.
Ta ce alakanta jam’iyyun da ta’addanci ba tare da sahihiyar shaida ba babban kuskure ne da ke lalata dimokraɗiyya kuma yana iya haifar da tashin hankali.
Don haka gwamnatin Nijeriya ta yi kira ga mahukuntan kasar Canada su gaggauta janye wannan kuskuren tare da kaucewa irin wadannan abubuwa da ka iya haifar da matsala ga diflomasiyya.
