Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnatin Tinubu za ta bullo da tsarin da zai rage farashin maganin...

Gwamnatin Tinubu za ta bullo da tsarin da zai rage farashin maganin da talakawa ke saye idan sun je asibiti

Gwamnatin Nijeriya ta amince da sabon tsari mai suna Medipool, wanda ake sa ran zai rage farashin magunguna da sauran kayan amfanin jinya a asibitoci ga ‘yan kasar.

Wannan na daga cikin muhimman matakan da aka cimmawa a zaman majalisar zartarwa ta tarayya da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Ministan lafiya Farfesa Ali Pate, ya bayyana cewa Medipool wata hadaka ce da za ta rika sayen kayan kiwon lafiya ta hadin guiwa domin samun farashi mai sauki, tare da samar da muhimman magunguna da kayan kiwon lafiya a fadin Nijeriya.

A cewarsa, an kirkiro Medipool ne domin hada bukatun cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da asibitocin tarayya, don bai wa gwamnati damar amfani da karfin sayayya mai yawa wajen rage kudin zuwa asibiti.

RELATED ARTICLES

1 COMMENT

  1. Qaryar Banza, abin da kuke fada ma Duniya daban abin da kuma kuke yi a bayan fage daban. Mu Talakawan Nigeria mun san cewar Allah yana tare da mu, kuma munyi Imanin ba zai kunyatar da mu ba Insha’allahu. Don haka wata Shari’ar sai a Lahira

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata