Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kafin ƙarshen shekarar 2025 za ta fara raba rancen kuɗi ba tare da ruwa ba ga manoma da kuma masu kananan sana’o’i a faɗin Nijeriya.
Shugaban shirin Government Enterprise and Empowerment Programme (GEEP) na kasa, Hamza Ibrahim Baba, ne ya bayyana haka a Kaduna yayin wani taro da wakilan ƙungiyoyin ƴan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a sashen kasuwanci suka yi.
Ya ce kowane mutum zai iya karɓar rancen har zuwa Naira 100,000, a ƙarƙashin shirin FarmerMoni, wanda aka shirya domin tallafawa ƙananan manoma da ke aikin kiwon kaji, kiwon kifaye, kiwon dabbobi da kuma noma.
Ya ce kuɗin za su taimaka wajen sayen taki, dabbobi, magungunan da sauran kayan aiki na noma.
Hamza Baba ya bayyana cewa shirin GEEP na ƙarƙashin ma’aikatar harkokin jin kai da rage talauci, kuma yana daga cikin muhimman shirye-shiryen rage radadin talauci ga ƴan Nijeriya.

I am a farmer