Dandalin gwamnonin jam’iyyar APC ta goyi bayan kafa ‘yan sandan jihohi kamar yadda gwamnan jihar Benue Hyacinth Alia ya bayar da shawara.
Kungiyar ta kuma yi alkawarin goyon bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a yunkurinsa na tunkarar kalubalen tsaron kasar nan.
Kungiyar ta bukaci gwamnoni da su kare jihohinsu ta hanyar amfani da jami’an tsaron al’umma.
Bayan ganawar sirri ta sa’o’i uku da suka yi, shugaban dandalin kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa gwamnonin na duba batun samar da ‘yan sandan jihohi ne bisa shawarar gwamnan Benue.
Wannan na zuwa ne yayin da kungiyar gwamnonin Nijeriya suka yi wani taron gaggawa a Abuja kan kalubalen matsalar tsaron kasar.
Duk da cewa ba a bayyana ajandar taron ba, an ga mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu, da ministan tsaro Mohammed Badaru a wurin taron.
