Gwamnonin jihohin Nijeriya 36 sun amince da rusa shingen kan tituna da kuma haraji da ake karba ba bisa ka’ida ba a fadin tarayya.
Gwamnonin sun yanke shawarar ne bayan taron kungiyar gwamnonin Nijeriya a Abuja wanda aka kammala da safiyar Alhamis.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya karanta sanarwar bayan taron, ya ce gwamnonin sun kuduri aniyar wargaza duk wasu baragurbin shingayen kan tituna da kuma haraji da ake karba ba bisa ka’ida ba wadanda ke haddasa tashin farashin abinci a kasar.
