Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuGwamnonin PDP sun gargadi Wike kan yunkurin kawo cikas ga babban taron...

Gwamnonin PDP sun gargadi Wike kan yunkurin kawo cikas ga babban taron jam’iyyar

Kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta yi gargaɗi ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu mambobin jam’iyyar kan yunkurin da zai iya lalata babban taron jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 ga Nuwamba, 2025.

Hakan na cikin sanarwar bayan taron gwamnonin karo na bakwai da aka gudanar a Gusau, Jihar Zamfara, ranar Asabar, 23 ga Agusta, 2025.

A cewar rahoton gidan talabijin na Channels, gwamnonin sun sake nanata goyon bayansu ga ƙudirin kwamitin zartarwa na ƙasa NEC na PDP karo na 101 da aka gudanar a watan Yuli, wanda ya amince da shirin babban taron jam’iyyar.

Taron na Gusau, ƙarƙashin jagorancin gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya kuma tattauna kan halin da ƙasar ke ciki, matsalolin tsaro, raguwar darajar dimokuraɗiyya, da shirye-shiryen babban taron PDP mai zuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata