Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedGwarzon aikin jarida ya cika 67: Tarihin hikima da jagorancin Dan Malikin...

Gwarzon aikin jarida ya cika 67: Tarihin hikima da jagorancin Dan Malikin Lafiya, Yusuf Sarki Muhammad

Daga Muhammad Aliyu Mustapha

A yau muna murnar zagayowar ranar haihuwar babban jigo a masana’antar watsa labarai—Alhaji Yusuf Sarki Muhammad, wanda aka fi sani da sarautarsa ta gargajiya, wato Dan Malikin Lafiya.

Yusuf Sarki Muhammad dai shahararren masanin aikin jarida ne, kwararre a fannin sadarwa, kuma ga shi fitaccen jagora abin koyi a harkar jarida ta zamani.

Duk wanda ya san Yusuf Sarki, zai shaida cewa shi tamkar wata “makaranta ce sukutum-da-guda” idan aka yi la’akari hikimarsa da kuma kwarewarsa a aiki.

Ta yin amfani da kamfaninsa, wato: ‘Actuality and Clips’ da ke Kaduna, Dan Malikin Lafiya ya kwashe shekaru yana rainon matasan ‘yan jarida da ma’aikatan kafafen yada labarai, inda yake koya musu dabarun aikin rediyo da talabijin kai har ma da kafafen sada zumunta na zamani.

Irin zurfin da Yusuf Sarki ya yi a harkar watsa labarai da kuma fahimtarsa ga wannan rayuwar ta duniyar sun sa ya zama tamkar wani babban rumbun ilimi ga duk mai kishirwar kwarewa da hidimtawa kasa. Dan Malikin Lafiya ya shahara da kwarewa bakin aiki da jajircewa wajen kiyaye dokokin tsarin aiki, don tsira da mutunci.

Yawancinmu muna cin moriyar sana’o’inmu ne sakamakon tarbiyya da jagorancinsa; ya nuna mana sirin wannan sana’a kuma ya dasa mana kishin aikin. Mu ne wadanda suka fi amfana da yalwar iliminsa, kuma muna alfaharin dorewar wannan gado nasa.

Muna addu’ar Allah Ya ci gaba da ba shi lafiya da arziki da tsawon kwana; Ya kuma ci gaba da kwararo masa albarkarSa ba tare da yankewa ba har abada. Amin!

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata