Tuesday, April 7, 2026
HomeSiyasaHadakar da nake sha'awa ita ce yaki da yunwa da Talauci a...

Hadakar da nake sha’awa ita ce yaki da yunwa da Talauci a fadin Nijeriya

A yayin da ake ci gaba da rade-radin yiwuwar hadaka tsakanin jiga-jigan ‘yan adawa don tunkarar shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya ce shi yaki da yunwa, fatara, da mummunan yanayin kiwon lafiya da ilimi a Nijeriya shi ya ke sha’awar yi.

Obi ya bayyana haka ne bayanda ya ziyarci Bishop na cocin Anglican Diocese na Kubwa a Abuja a ranar Litinin dinnan inda ya jaddada cewa ba shi da burin samun wani matsayi.

Peter Obi dai shi ne ya zo na uku bayan Shugaba Tinubu da Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP a zaben 2023, inda da dama ke ganin cewa hadakar hadin gwiwa tsakaninsa da Atiku da sauran jam’iyyun adawa za ta iya kai bantensu a zaben shugaban kasa na 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata