Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuHar yanzu Bello Turji bai ajiye makamansa ba - Hedikwatar tsaron Nijeriya

Har yanzu Bello Turji bai ajiye makamansa ba – Hedikwatar tsaron Nijeriya

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa dan bindiga Bello Turji ya mika wuya ga sojoji.

Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar Markus Kangyebya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja yayin wani taron manema labarai kan ayyukan rundunar.

Bello Turji, wanda ake nema ruwa a jallo, na gudanar da ayyukan sa na ta’addanci ne musamman a jihohin Zamfara da Sokoto, kuma ana zarginsa da kai hare-hare da dama a yankin Arewa maso yamma.

A kwanakin baya wasu rahotanni sun ce Turji ya ajiye makamansa tare da sakin mutane 32 da aka yi garkuwa da su, bayan wani shirin sulhu da malamai suka jagoranta a Zamfara.

Hedikwatar tsaron ta ce har yanzu babu wani tabbaci kan wannan ikirari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata