Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuHar yanzu gwamnatin Nijeriya tana biyan tallafin man fetur a boye –...

Har yanzu gwamnatin Nijeriya tana biyan tallafin man fetur a boye – Babachir Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya Babachir David Lawal ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana cewa ba zai iya aiki da ita ba, kuma da ya samu mukami da tuni ya yi murabus.

A hirarsa da gidan talabijin na Channels, Babachir ya zargi gwamnatin da nuna son kai da yawan baiwa ’yan kabilar Yarbawa mukamai, wanda hakan a cewar sa rashin adalci ne.

Ya kuma yi korafi kan manufofin tattalin arziki, musamman cire tallafin man fetur tun watan Mayun 2023, tare da cewa har yanzu ana biyan tallafin man fetur a boye, kuma ’yan Najeriya ba sa amfana da cirewar da aka yi.

Lawal ya ce tsarin mulkin Tinubu ya yi tasiri wajen haifar da hauhawar farashi da wahala ga talakawa a Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata