Rundunar sojin saman Nijeriya ta kaddamar da hare-hare na musamman kan sansanonin ‘yan bindiga, da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, wanda ya lalata wani muhimmin sansanin ’yan ta’adda a yankin.
A cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar a shafinsa na X a ranar Asabar, ya ce harin ya gudana ne a ranar 14 ga Nuwamba 2025 ta hannun bangaren sojin sama na Operation Fansan Yamma.
Ejodame ya bayyana cewa luguden wutar ya biyo bayan cikakken binciken leken asiri da sa ido da ya tabbatar da tarin ’yan ta’adda da kuma dabbobin da suka sace a wani dutse da suke amfani da shi wajen boyewa da adana makamansu.
