DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeBabban LabarinmuHarin jiragen soji bisa kuskure ya yi ajalin sama da mutane 50...

Harin jiragen soji bisa kuskure ya yi ajalin sama da mutane 50 a wata kasuwa da ke kan iyakar Borno/Yobe

Aƙalla mutane 56, galibinsu ‘yan kasuwa, suka rasu wasu da dama suka jikkata sakamakon wani harin jirgin sama da ake zargin an yi kuskure a kasuwar mako-mako ta Jilli da ke iyakar jihohin Borno da Yobe.

Jaridar Daily Trust ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a kasuwar Jilli, wadda ke tsakanin ƙananan hukumomin Gubio a jihar Borno da Geidam a Jihar Yobe.

An ce harin ya faru ne yayin wani samame da sojoji ke yi kan ‘yan ta’addan Boko Haram, amma harin ya kauce daga inda aka nufa, ya afkawa fararen hula.

Shaidu sun ce jiragen yaƙi huɗu ne suka kai harin da misalin ƙarfe 2 na rana yayin da kasuwa ke cike da jama’a daga yankuna daban-daban.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa ya ƙirga gawarwaki 56 da kansa, sannan ya taimaka wajen kai wasu da suka jikkata zuwa asibitin ƙwararru na Geidam.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata