Wasu bayanai da babban bankin Nijeriya CBN ya fitar, sun nuna cewa yawan kudaden da ‘yan Nijeriya ke kashewa wajen gudanar da gidajensu ya ragu da akalla Naira tiriliyan 14.
Bayanan da bankin ya fitar a shekarar 2024, sun nuna cewa an samu wannan sauyi ne sakamakon hauhawar farashin kayayyakin amfanin yau da kullum.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa hauhawar farashin a shekarar ta 2024 na da alaka ta kai tsaye da cire tallafin man fetur, sai kuma rashin samun tsayayyen farashi a kasuwar canjin kudade.
Hakan dai ya tilastawa ‘yan Nijeriya da dama mayar da hankali kan gabatar da bukatun da suka zama wajibi gare su, bayan hakura da wasu abubuwan, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
