Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuHedikwatar tsaron Nijeriya ta gayyaci sojojin da ake zargi da sakaci wajen...

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta gayyaci sojojin da ake zargi da sakaci wajen sace daliban jihar Kebbi don ci gaba da bincikensu

Hedkwatar tsaron Nijeriya ta gayyaci dukkan sojojin da aka janye daga Government Girls’ Comprehensive SSS, Maga, a Danko/Wasagu, Jihar Kebbi, kafin sace dalibai 26 da ‘yan ta’adda suka yi domin ci-gaba da bincike.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa hedikwatar tsaro ta kaddamar da bincike kan dalilin janyewar sojojin da gaggawa.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kutsa makarantar ne ranar 17 ga watan Nuwamba, inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Makuku, sannan suka yi awon gaba da dalibai 26, daga ciki biyu sun tsere, ragowar 24 kuma suna hannun masu garkuwa har sai da gwamnatin tarayya ta sulhunta aka sako su.

Gwamna Nasir Idris ya bukaci a binciki dalilin janyewar sojojin duk da cewa jihar ta samu bayanan leken asiri da suka nuna cewa makarantar na cikin hadari.

Hakazalika, hakimin Maga, Muhammad Dantani, ya tabbatar da cewa sojojin sun bar wajen kimanin ƙarfe 1 na dare, kafin harin ya fara karfe 1:30 zuwa 3:30 na safe ba tare da turjiya ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata