Sunday, April 5, 2026
HomeUncategorizedHukumar Hisbah a jihar Kano takama mota dauke da barasa

Hukumar Hisbah a jihar Kano takama mota dauke da barasa

 Hisbah a Kano ta kama mota makare da barasa 

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sanar da kama wata babbar mota makare da kwalaben barasa.

Hukumar ta kama motar a hanyar Zariya, ta kuma kama direban motar da wasu mutane biyu. 

Babban Daraktan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Alhaji Abba Sufi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Malam  Ibrahim-Fagge ya sanya wa hannu a Kano.

“ Yace Motar da ke dauke da kwalabe daban-daban na barasa sama da 24,000 an kwace daga hannun ‘yan sumogal a hanyar Zariya da tsakar dare.

Jami’an Hisbah a jihar sun himmatu wajen yaki da shan miyagun kwayoyi da fasakwaurin barasa da sauran abubuwa masu sa maye a cikin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata