Hukumar yaki da cin hanci mai zaman kanta (ICPC) ta gabatar da sabbin tuhume-tuhume guda tara kan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan zargin rashawa, cin zarafin mukami da kuma almundahana.
Lauyan El-Rufai, Ukpong Abang, ya ce an gyara tuhume-tuhumen ne a kotun jihar Kaduna, inda aka cire wani da ake kara tare da shi, tare da barin tsohon gwamnan shi kadai a shari’ar.
Ya kara da cewa an mika musu sabbin tuhume-tuhumen ne a kotu a ranar Litinin, wanda hakan ya sa ba a ci gaba da sauraron shari’ar ba, domin su fara nazarin su kafin daukar mataki.
Kotun ta saurari bukatar beli da aka shigar, sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar Talata, 14 ga Afrilu, domin yanke hukunci kan bukatar belin.
A cikin tuhume-tuhumen, ICPC ta zargi El-Rufai da bai wa wani kamfani kwangilar jirgin kasa ta sama da darajar naira biliyan 11 ba tare da aiwatar da aikin ba, da kuma karbar kudin fansho fiye da yadda doka ta tanada.
Sauran tuhume-tuhumen sun hada da zargin karkatar da sama da dala miliyan daya na bashin Bankin Duniya, karya dokokin saye da sayarwa, da kuma ba wasu na kusa da shi fifiko a harkokin gwamnati kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
