DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
HomeUncategorizedHukumar ICPC za ta bi diddigin wasu ayyuka a jihar Kano

Hukumar ICPC za ta bi diddigin wasu ayyuka a jihar Kano

 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC ta soma bin diddigin wasu ayyukan ci gaban al’umma na mazabun ‘yan masalisa da na kananan hukumomi a jihar Kano domin tabbatar da bin ka’ida

Ayyuka 99 ne za ayi a mazabun ‘yan majalisa, sai wasu manyan ayyuka bakwai a kananan hukumomi 44 na jihar, wadanda za su lakume kudaden su suka kai naira biliyan 41.

Shugaban hukumar ICPC a Kano Barista Ibrahim Garba Kagara, ya ce za su sanya ido akan yadda za a gudanar da ayyukan domin tabbatar da cewa ba a aikata wata almundahana ba, kuma an gudanar da su kamar yadda aka tsara domin amfanin al’umma.

Hakama ya bukaci al’ummar da za a yiwa wadannan ayyuka da su sanya ido kuma su kai rahoton duk wata rufa-rufa ko badakala da suka ga ana shirin aikatawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata