Sunday, April 5, 2026
HomeBabban LabarinmuHukumar tace finafinai ta jihar Kano ta haramta "KAUYAWA DAY a jihar

Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta haramta “KAUYAWA DAY a jihar

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta sanar da haramta bikin “KAUYAWA DAY” da ake ganin wasu ‘yan mata na sanya kananan kaya tare da yin rawar nuna fitsara.

Haka kuma, hukumar ta dakatar da dukkanin dakunan taro na gidajen biki na musamman, wato Event Centers har zuwa lokacin da za a cimma matsaya kan dokokin da aka kafa musu domin tsabtacewa ba tare da saba dokokin addini ko gurbata al’ada ba.

Shugaban hukumar, Abba El-mustapha ne ya bayyana hakan, a yayin wata ganawa ta musamman da manema labarai, jim kadan bayan wani taron gaggawa da hukumar ta gabatar a kan lamarin bikin KAUYAWA DAY.

Abba El-Mustapha ya kara da cewa, wannan mataki ya zama dole duba da irin korafe-korafen da suke karba da kuma jan hankali daga wajen malamai da wasu masu fada a ji a jihar ta Kano.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata