Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuHukumomi a Nijeriya sun karbi 'yan kasar 139 daga jamhuriyar Nijar

Hukumomi a Nijeriya sun karbi ‘yan kasar 139 daga jamhuriyar Nijar

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA ta karɓi ‘yan ƙasar 139 da suka dawo daga Agadez, Jamhuriyar Nijar, a ci gaba da kokarinta na dawo da ‘yan Nijeriya da suka makale a wasu kasashen.

Wadanda suka dawo sun iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano da yammacin ranar Talata, 29 ga Yuli, 2025, ta jirgin Sky Mali da ya sauka misalin ƙarfe 7:57 na dare.

A cewar ofishin NEMA na jihar Kano da ya fitar da bayani a shafinsa na X ranar Alhamis, waɗanda suka iso sun haɗa da manya maza 22, manya mata 52, yara maza 33 da kuma yara mata 32.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata