Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuIfeanyi Okowa da ya yi wa Atiku Abubakar takarar mataimakin shugaban kasa...

Ifeanyi Okowa da ya yi wa Atiku Abubakar takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 a PDP ya fice daga jam’iyyar ya koma APC

Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da mataimakinsa, Monday Onyeme, sun fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party wato PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress ta APC.

Sanata James Manager ne ya sanar da hakan a birnin Asaba jihar Delta, jim kadan bayan wani taro da ya dauki tsawon sa’o’i shida a gidan gwamnati dake Asaba.

Sanata James ya bayyana cewa, dukkanin ‘ya’yan jam’iyyar PDP na jihar da suka hada da gwamna, tsohon gwamna Okowa, shugaban majalisar dokoki, shugaban jam’iyyar na jihar, shugabannin kananan hukumomi da sauran su sun amince su koma APC.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata