Monday, April 6, 2026
HomeUncategorizedIna sane da mawuyacin halin da 'yan Nijeriya ke ciki inji shugaban...

Ina sane da mawuyacin halin da ‘yan Nijeriya ke ciki inji shugaban kasa Bola Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce ya fahimci irin halin kuncin da talakawan kasar suka shiga ta dalilin cire tallafin man fetur, inda ya tabbatar da cewa an dauki matakin ne don kasar ta cigaba da kuma gina kyakkyawar rayuwa ga ‘yan kasa.

Shugaba Bola Tinubu da ya karbi bakuncin tsoffin gwamnoni 18 da suka yi zamani tare a shekarar 1999 ya ce akwai bukatar ‘yan Nijeriya su kara hakuri da halin da suke ciki.
Ya tabbatar da cewa an yi tsari mai kyau domin rarraba tallafin da zai rage radadin da ‘yan Nijeriya ke ciki.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata