Monday, April 6, 2026
HomeBabban LabarinmuINEC ta gargadi masu yakin neman zabe kafin lokacin da doka ta...

INEC ta gargadi masu yakin neman zabe kafin lokacin da doka ta tanada 

Hukumar zaben Nijeriya INEC, ta bayyana damuwarta kan yadda jam’iyyun siyasa da ‘yan takara ke fara yaƙin neman zaɓe tun kafin lokacin da doka ta kayyade a shirye-shiryen zaɓen 2027.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana haka a wani taron tattaunawa da hukumar ta shirya a Abuja, inda ya ce dokar zaɓe ta 2022 ta kayyade kwanaki 150 kafin zaɓe a fara gangamin neman goyon baya.

Sai dai ya bayyana cewa dokar bata tanadi hukunci ga masu karya wannan doka ba, lamarin da ya kira babban kalubale ga hukumar.

Yakubu ya ce wannan hali na yaƙin neman zaɓe tun da wuri na kawo cikas wajen bibiyar kuɗaɗen kamfe, kasancewar ‘yan takara da magoya bayansu na kashe makudan kuɗaɗe ba tare da wani tsarin doka da zai kula da su ba.

A nasa jawabin, tsohon shugaban hukumar, Farfen Attahiru Jega, ya ce wannan dabi’ar na iya zama babbar barazana ga sahihancin zaɓe, inda ya kira ta barazana ga dimokuraɗiyya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata