Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fitar da jadawalin babban zaben 2027, inda ta sanar da cewa za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Tarayya ranar 20 ga Fabrairu, 2027, yayin da zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi zai gudana ranar 6 ga Maris, 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja, yana mai cewa hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zaben bisa tanadin kundin tsarin mulki da Dokar Zabe ta 2022.
Ya ce sanar da jadawalin ya dace da sharuddan doka da ke bukatar a fitar da sanarwar zabe akalla kwanaki 360 kafin ranar zabe, tare da jaddada cewa ikon sanya ranar zabe na hannun INEC ne kawai.
Hukumar ta kuma ce cikakken jadawalin ayyuka, ciki har da lokacin gudanar da zaben fidda gwani da fara yakin neman zabe, an wallafa su a shafinta, tare da umartar kwamishinonin zabe na jihohi 36 da na FCT su sanar da jama’a a mazabunsu.
